Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya NIMET ta ce za a samu tsananin zafi da kwallewar rana daga Asabar 22 zuwa Litinin 24 ga Fabrairu 2025.
Hukumar ta ce za a samu hasken tare da yanayin Hazo a wasu sassan Arewacin kasar, yayin da za a samu kadawar Iska a wasu jihohin Arewa ta Tsakiya da Kudancin kasar.
Daga cikin jihohin da za a samu yanayin Hazo da Rana akwai Nassarawa sai Plateau da Kogi da Benue sai birnin Tarayya Abuja.
A kudancin kasar kuwa za a samu hadari da tsawa a jihohin Lagos, Delta sai Cross River.
Category
Labarai