Rundunar sojin Nijeriya ta sake tabbatar wa ‘yan kasar cewa tana ci gaba da laluben ƙasurgumin ɗan bindigan nan Bello Turji, kuma za ta cimmai ba da jimawa ba.
Babban Hafsan Sojojin Nijeriya mai kula da aikace-aikace, Manjo Janar Emeka Onumajuru ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin.
Wannan dai ba shi ne karon farko da sojojin Nijeriya ke alkawarin kamo bello Turji da ya dade yana addabar yankin Arewa maso Yamma ba.
Category
Labarai