‘Yan sanda sun yi ajalin ‘yan bindiga 11 tare da ceto mutane 85 da aka sace a Katsina

 



Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta ce ta halaka ‘yan bindiga 11 tare da ceto mutane 85 da aka sace a watan Janairun 2025.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan, DSP Abubakar Aliyu, ya fitar a madadin kwamishinan ‘yan sandan, Abubakar Musa.

Ya ce an kama mutane 45 da ake zargi da aikata manyan laifuka yayin da aka kwato dabbobin da aka sace 213 a lokacin da ake bincike.

Aliyu ya kara da cewa, an kwato harsashi guda hudu na AK-47, babura uku,ta re da  kama mutane 45 da ake zargi da aikata manyan laifuka guda 52, wadanda suka hada da fashi da makami, kisan kai, garkuwa da mutane, da sauran su.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp