![]() |
Police |
Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama wasu mutane uku da ake zargi da lalatawa da kuma satar wayoyin na'urar raba lantarki a Wuro Dole da ke karamar hukumar Girei a jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Suleiman Nguroje ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Yola, babban birnin jihar.
Ya ce kamen ya biyo bayan sahihan bayanai da suka samu daga wata majiya mai tushe, wanda ya kai ga cafke wasu mutane uku da ake zargi da satar wayoyin wutar lantarki da ke samar da wuta a sassan Girei.
Wadanda ake zargin, Rabiu Ali mai shekaru 28, sai Muhammad Musa mai shekaru 42, da Abubakar Usman mai shekaru 18, sun hada baki da wasu mutum uku waɗanda har yanzu ana nemansu.