Kididdiga ta nuna cewa yawan data da 'yan Nijeriya suka kone ta karu zuwa terabytes 973,455 a cikin watan Disamban 2024, abinda ke nuna cewa an samu karin kashi 36.5 idan aka kwatanta da shekarar 2023 da 'yan Nijeriya suka yi amfani da data terabytes 713,200 a cikin watan Disamban 2023.
Adadin datar ya kai gida milyan 998.79 kenan.
A cikin wata kididdiga da hukumar sadarwa ta Nijeriya NCC ta fitar, ta ce an samu kari kashi 10.75 wajen amfani da yanar gizo a kasar cikin watan Disamban 2024.
Category
Labarai