Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya Ola Olukoyede, ya ce 'yan Nijeriya na tsinuwa ga cin hanci amma kuma su rika goyon bayan gurbatattun shugabannin da aka gurfanar a gaban kotu.
Olukoyede ya ce kasar nan za ta fita daga kangin da take ciki idan har kowane dan kasa zai yaki cin hanci a duk inda aka aikata shi.
Shugaban na EFCC ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugabannin cibiyar naƙaltar sadarwa lokacin tarzoma suka kai masa a Abuja.
Category
Labarai