![]() |
Rundunar ‘yan sandan jihar Benue ta tabbatar da sace dalibai mata 4 na jami’ar aikin gona ta gwamnatin tarayya da ke Makurdi.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Benue, CSP Sewuese Anene, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da gidan talabijin na Channels, inda ya ce an fara gudanar da bincike tare da nemo inda suke.
Wasu majiyoyi a kusa da jami'ar sun ce wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da daliban ne a harabar jami’ar da misalin karfe 8:30 na dare, lamarin da ya haifar da firgici ga daliban.
Yace daliban da aka yi garkuwa da su sun hada da, Emmanuella Oraka, Fola, Susan da kuma Ella.
A halin da ake ciki dai labarin sace daliban ya haifar da zanga-zanga daga daliban da suka zagaye makarantar inda suka bukaci mahukuntan makarantar su dauki matakin gaggawa.