Kungiyar "Independent Hajj Reporters" mai sanya ido kan harkokin aikin hajji ta yi kira ga hukumar alhazzan Nijeriya da ta mayar wa maniyyata aikin hajjin bana naira N437,000 kowannensu, bayan da aka samu saukar farashin dala a kasuwar canji.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar, ta ce binciken da ta yi akan bayanan kudin aikin hajjin 2025 da hukumar NAHCON ta fita, ta gano cewa ya kamata kowane maniyyaci a mayar masa da rarar kudin da ya biya.
Sai dai a martanin da suka mayar, bangaren yada labarai na hukumar NAHCON sun bayyana cewa, sabanin fahimtar kungiyar IHP duk wani sauyi da aka samu a canjin kudi bayan an kayyade kudin aikin hajji, kai tsaye ba ya nufin za a mayar wa mahajjata kudin.
Bangaren yada labaran sun kara da cewa hukumar NAHCON ta yi alkawalin bin ka'ida wajen mayar wa mahajjata kudin su idan aka samu wani ragi.
Category
Labarai