Wata babbar mota tirela da ta kwace ta yi ajalin mutane da dama a Kano


Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun rasu yayin da wasu suka jikkata bayan da wata tirela ta kwace akan gadar Muhammad Buhari da ke Kano kan titin Mariri zuwa Unguwa Uku.

Hatsarin ya faru ne sanadiyar katsewar birkin motar wadda ke kan hanyar zuwa kudancin Nijeriya, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.

Wani shaidar gani da ido ya ce motar ta kwace ne yayin da direban yake kokarin wucewa kan mararrabar da ke kasan hanyar wadda za ta wuce zuwa titin Ring Road kuma ta hada da babban titin Zaria.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp