Ma’aikatan agaji a birnin Alaska na kasar Amurka na neman wani karamin jirgin sama na kasuwanci da ya bata a ranar Juma’ar nan tare da mutane 10 a cikinsa, kamar yadda hukumomin yankin suka ce.
Rundunar yan sandan jihar ta Alaska ta ce jirgin Bering Air Caravan dauke da fasinjoji tara da matukin jirgi daya, ance ya bata ne tun ranar Alhamis bayan tashi daga Unalakleet zuwa Nome da karfe 4:00 na yamma agogon Alaska.
Category
Labarai