Wani dan Majalisar wakilan Nijeriya daga PDP ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

 

Majalisar wakilan Nijeriya

Dan majalisar mai wakiltar mazabar Jaba/Zango Kataf a jihar Kaduna, Amos Magaji, ya shirya sauya sheka ne bisa rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya.

Kakakin majalisar Tajudeen Abbas wanda ya jagoranci zaman majalisar a ranar Talata ya karanta wasikar sauya shekar Magaji a zauren majalisar.

Magaji ya ce rikicin da haryanzu ba a warware a PDP ba tun daga matakin kasa har zuwa jiha ya sa ba zai iya zama a cikin jam'iyyar ba.

Magaji dai shi ne dan jam’iyyar PDP na uku da ya koma APC tun bayan kaddamar da majalisar ta 10 bayan Chris Nkwonta da Eriatheke Ibori-Suenu, daga jihohin Abia da Delta.

Da yake nuna adawa da sauya shekar, shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, ya bukaci kakakin majalisar da ya ayyana kujerar dan majalisar na Kaduna a matsayin wadda babu kowa kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp