Tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido ya bayyana damuwarsa kan yadda malaman addini shiga harkokin siyasa, indaj ya bayyana cewa a yanzu malamai suna da tasirin gaske a kan masu zabe da harkokin siyasa

 

Sule Lamido


Sule Lamido ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ke yawo, wanda ke nuna lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sheikh Yusuf Sambo Rigachikun a Kaduna sakamakon rasuwar babban dansa.


Tsohon ministan harkokin wajen ya koka da yadda malaman addini suke ci gaba da mamaye fagen siyasa, inda suke fitowa karara suna kamfen ga ‘yan takara tare da jagorantar mabiyansu kan wadanda za su marawa baya, ya kara da cewa duk da albarkar kasancewarsu shugabannin addini, malamai yanzu suna tallafawa masu neman mulki.


A cewar sa kamata ya yi malamai su tsaya a matsayinsu na malamai, 'yan siyasa su tsaya a matsayinsu na 'yan siyasa domin samun daidaito da adalci ga al'ummar da ake jagoranta.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp