Tsaro da tattalin arziki sun inganta a lokacin ina shugaban Nijeriya - Muhammad Buhari




Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa tsaro da tattalin arzikin kasar nan sun inganta sosai a tsawon shekaru takwas da yayi yana mulki.

Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Larabar da ta gabata yayin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Katsina a gidan sa dake Daura a jihar Katsina.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa ya gaji mummunar tattalin arziki da kalubalen tsaro daga jam’iyyar PDP da ta shafe shekaru 16 tana mulki.

Buhari, ya tabbatar da cewa dabarun gwamnatinsa sun yi nasarar magance wadannan kalubale, wajen dakile ta’addanci da matsalolin tattalin arziki.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp