Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sauke Aisha Maikudi mataimakiyar shugabar jami’ar Abuja, wadda a yanzu ake kira da Jami’ar Yakubu Gowon.
An sanar da sauke Aisha Maikudi sa’o’i kadan bayan da ta jagoranci bikin yaye dalibai da suka kammala karatun digiri a makarantar.
Dama dai ana ta cece-kuce game da nadin nata inda wasu malaman jami'ar ke cewa, ta hau wannan mukamin ba bisa ka'ida ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.