Sojojin Nijeriya sun halaka ‘yan bindiga da dama, tare da lalata maboyarsu a dajin Sakkarawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto

 

CDS Christopher Musa

Rundunar hadin gwiwa ta Operation FANSAR YAMMA tare da hadin gwiwar ‘yan sakai sun halaka tare da lalata wata maboyar 'yan bindiya wadda akafi sani da "Dan Dari Biyar” da ke dajin Sakkarawa a yammacin Sabon Birni a jihar Sokoto.

Wasu majiyoyi sun tabbatarwa da mai sharhi kan al'amuran tsaro Zagazola Makama cewa an halaka wasu ‘yan bindiga a yankin yayin da wasu suka yi nasarar tserewa da munanan raunuka a harin da aka kai a ranar 17 ga Fabrairu, 2025. 

Wani wanda aka ceto daga cikin wa'yanda 'yan bindigar sukai garkuwa da shi a kwanakin baya, bayan ya shafe watanni biyu a tsare a sansanin ‘yan bindigar, ya bayyana irin halin da ya shiga da irin wahalar da ya sha a hannun su. 

Sai dai majiyar ta ce jami'an tsaro sun zafafa kai hare hare kan 'yan ta'addan da suka tsere tare da tabbatar da cewa sun share yankin gaba daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp