Sojojin Nijeriya sun ceto mutane 59 da aka yi garkuwa da su daga maboyar 'yan bindiga

CDS Christopher Musa

A ranar 15 ga Fabrairu, sojojin da ke aikin Operation Fansan Yamma da ke ci gaba da kai hare hare a garuruwan Chikun, Kajuru da Kachia, sun kubutar da mutane 50 da aka yi garkuwa da su, da suka hada da maza 22, mata 25 da yara uku.

Jaridar PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa, rundunar hadin gwiwa daga shiyya ta daya da kuma jami'an ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro NSA sun karbi wadan da suka tsira  bayan an kubutar da su daga hannun ‘yan ta’addan da suka yi garkuwa da su.

Rahoton  ya tabbatar da kai mutanen da aka kubutar zuwa asibitin hukumar 'yan sanda na jihar Kaduna domin kula da lafiyar su.

Kazalika jami'an sojin sun kuma ceto wasu mutane tara da aka yi garkuwa da su - maza biyu, mata biyar da kuma kananan yara biyu,da tuni  an wuce da su zuwa asibiti  domin duba lafiyar su.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp