Shugaba Trump na Amurka ya hana kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP) daukar rahotanni daga fadar White House

Donald Truph

 

A cewar kamfanin na AP, fadar White House ta yi gargadin cewa idan AP basu daidaita salonsu da umarnin Shugaba Donald Trump na canza sunan Tekun Mexico zuwa "Gulf of America," za a hana su shiga.

Editan AP Julie Pace ta yi Allah wadai da matakin, tana mai cewa hakan ya saba wa ‘yancin ‘yan jarida.

Ita ma kungiyar masu aiko da rahotanni ta fadar White House WHCA ta soki matakin, inda ta bayyana cewa haramta wa 'yan jarida yin aikinsu ba abu ne da ba za a amince da shi ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp