Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci gwamnan jihar Kano Abba Yusuf da ya magance rikicin filaye da Jami'ar Bayero ke yi da al'ummomin da suke makwabtaka.
Tinubu wanda ya samu wakilicin ministar kasa a ma'aikar ilimi Farfesa Suwaiba Ahmed ya yi wannan kiran ne a yayin bikin yaye dalibai karo na 39 da jami'ar ta gudanar.
Ya yi kira ga gwamnan da ya gaggauta bai wa makarantar takardun mallaka domin magance rikicin.
Category
Labarai