Shugaba Tinubu ya isa birnin Adis Ababa na kasar Habasha domin halartar taron kungiyar kasashen Afrika


Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya sauka birnin Addis Ababa, na kasar Ethiopia, domin halartar taron shugabannin kungiyar kasashen Afrika AU karo na 38.

Tinubu ya samu tarba daga wani jami'in gwamnatin kasar Habasha Eshetu Legesse, da ministan harkokin waje da babban jami'i a ofishin jakadancin Nijeriya na kasar Ambassador Nasir Aminu.

Shugaban ya kuma karbi bayanai akan taron da kuma nasarorin da kasar ta samu ta fannin diflomasiyya.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp