![]() |
Ganduje / Shugaba Tinubu |
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya dage cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi wa’adi na biyu na shekaru takwas a kan karagar mulki tsakanin 2023 zuwa 2031.
Ganduje da yake maida martani kan kalaman tsohon Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-rufa'i a ranar Talata a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar matasan Arewa na Tinubu a sakatariyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja, ya ci gaba da cewa ba za a sauya ka’idar mika mulki tsakanin Arewacin Nijeriya da Kudancin kasar ba don haka shugaba Tinubu zai yi shekaru takwas koda mulki zai dawo Arewa.
Gandujen ya yi tsokaci ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda yayi wa'adi biyu akan karagar mulki domin ya tabbatar da cewa shugaba Tinubu shima zai samu irin wannan gatan.