![]() |
SDP Chiarman Gabam |
Shugaban jam’iyyar SDP a Nijeriya, Shehu Gabam, ya ce tsauraran manufofin tattalin arzikin shugaban Bola Tinubu na iya zama babbar matsala a gare shi idan ya yi yunkurin sake tsayawa zabe a 2027.
Gabam da yake lissafo wasu daga cikin manufofin gwamnatin Tinubu a gidan talabijin na Channels, ya ce cire tallafin man fetur,karin kudin wutan lantarki, da karin kudin sadarwa na daga cikin abubuwanda ka iya ba shi matsala.
Ya kara da cewa Tinubu na bukatar ya sake duba wasu daga cikin manufofinsa, da bukatar ya sauya majalisar ministocinsa idan yana son ya ci zabe domin ba zai iya cin baze da irin wadannan manufofin ba.