Shugaba Bola Tinubu ya amince da a kashe naira biliyan 80 wajen fadada madatsar ruwa ta Alau a jihar Borno

 

Shugaba Tinubu

Ministan albarkatun ruwa Farfesa Joseph Utsev, ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan taron majalisar zartaswa ta kasa FEC a ranar Talata.

Utsev, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin ma’aikatun da ke kula da madatsun ruwa, ya bayyana cewa shugaban kasar ya amince da gyaran madatsar ruwa ta Alau, bayan tattaunawa da aka yi bisa bukatar hakan.

Kwamitin, wanda aka kafa a ranar 23 ga Satumba, 2024, ya hada da ministocin kudi, muhalli, ayyuka, yada labarai, da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a matsayin mambobi.

An kaddamar da kwamitin ne a ranar 2 ga Oktoba, 2024 da nufin tantance madatsun ruwa a fadin kasar tare da ba da shawarar ingantasu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp