SERAP ta yi karar babban bankin Nijeriya CBN kan karin kudin chaji na ATM

 

CBN

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci a Nijeriya ta yi karar babban bankin kasar CBN kan wasu sauye sauye na karin kudin cajin ATM da aka yi,da ta ce anyi shi ba bisa ka’ida ba.


A baya bayan nan ne dai CBN ya sanar da cewa, cire kudi a ATM din da ba bankin da mutum ke amfani da shi ba a yanzu za ta rika daukar naira 100 ga duk wanda ya ciri adadin kudin da ya kai naira dubu 20,000.


A karar da ta shigar mai lamba FHC/L/CS/344/2025 a ranar Juma’ar da ta gabata a gaban babbar kotun tarayya da ke jihar Legas, SERAP ta nemi kotun da ta yi duba kan matakin da CBN ya yanke na karin kudin cajin na ATM, wanda ta kira a matsayin rashin adalci, kuma ya saba wa tanadin dokar kasa.


SERAP na neman kotu da ta ba da sanarwar cewa matakin da CBN ya dauka na kara kudaden hada hadar kudi na ATM anyi shi ne ba bisa ka’ida ba, kuma ya sabawa tanadin sashe na 1 (c) da (d), 104, 105 da 127 (1) na dokar kasa ta tarayya da kuma kare hakkin al'umma ta 2018.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp