![]() |
Dabino |
Ofishin jakadancin Saudiyya da ke Abuja ya gudanar da wani biki a hukumance don raba tan 100 na dabino ga Nijeriya a wani bangare na ayyukan agaji da take yi duk shekara.
Shirin wanda cibiyar ba da agaji da jinkai ta Sarki Salman (KSrelief) ta dauki nauyin gudanarwa, na da nufin tallafawa iyalai masu karamin karfi a fadin kasar da kuma karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.
A yayin bikin, jakadan a Nijeriya Faisal bin Ibrahim, ya bayyana kwazon masarautar ta Saudiyya kan ayyukan jin kai.
Ya kuma bayyana godiyarsa ga Sarki Salman bin Abdulaziz da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman bisa goyon bayan da suke ba wa musulmi da al'ummomin da ba a fadin duniya.