Sama da yara 11,000 masu kananan shekarunsu aka yi wa rejistar JAMB - Shugaban hukumar JAMB Farfesa Oloyode



Shugaban hukumar zana jarabawar gaba da sakandire a Nijeriya Farfesa Ishaq Oloyede ya bayyana cewa sama da yara 11,553 masu kananan shekaru aka yi wa rejistar zana jarabawar JAMB ta shekarar 2025.

Oloyede ya bayyana hakan ne a yayin da yake duba wasu cibiyoyin da ake yi wa dalibai rejista.

A cewar Oloyede, zuwa yanzu dalibai 782,027 ne aka yi wa rejistar zana jarabawar a cikin kwana goma da suka gabata.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp