Ofishin jakadancin kasar Kanada a Nijeriya ya ce ya yanke shawarar kin bayani akan dalilin da ya sa aka hana wa babban hafsan sojoji Janar Christopher Musa visa da wasu manyan sojoji saboda dalilai na sirri.
Sai dai a martanin ministan cikin gida na Nijeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya ce babu dalilin da gwamnatin kasar za ta hana wa sojojin izinin shiga kasar.
Hakama mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana matakin a matsayin cin fuska ga Nijeriya.
Category
Labarai