Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce makamai 3,907 da ake bincike sun yi ɓatan dabo ne tun kafin Sufeta Janar na yanzu Kayode Egbetokun ya karɓi jagoranci.
Mai magana da yawun rundunar Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a cikin wani bayani da ya fitar, inda yace bata gari ne suka sace makaman lokacin hatsaniya.
Yace rundunar ta yi duk kokarinta wajen kwato makaman kuma tuni wasu suka dawo hannun rundunar.
Category
Labarai