![]() |
SP Abdullahi Haruna Kiyawa |
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama mutane 17 da ake zargi da shirya zanga-zanga a jihar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da maimagana da yawun rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Kiyawa ya fitar ranar Laraba a Kano.
Ya ce rundunar ta dauki matakan tsaro da suka dace domin dakile duk wani abu da ka iya haifar da rashin bin doka.
Kiyawa ya ce rundunar ta tura jami’anta zuwa wasu muhimman wurare a cikin birnin Kano domin hana zanga-zangar da kuma tabbatar da tsaron jama’a.