Gwamnonin jam'iyyar PDP sun nuna goyon bayansu ga Sunday Ude-Okoye a matsayin sakataren jam'iyyar na kasa.
A cewar jaridar Punch wasu magoya bayan ministan Abuja Nyesom Wike sun ce Samuel Anyanwu ne Sakataren PDP har zuwa ranar da aka yi babban taron jam'iyya na kasa.
Babbar jam'iyyar adawa na ci gaba da fama da rikicin cikin gida yayin da shekara ta 2027 ke karatowa.
Category
Labarai