Shugaban haramtacciyar Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafara(IPOB) Nnamdi Kanu ya nuna bukatar mai sharia'a Binta Nyako da ta kori karar da ke zargin sa a shari’ar da ke gudana tsakanin shi da gwamnati.
A Zaman kotun da ya gudana a babbar kotun tarayya da ke Abuja a safiyar Litinin dinnan Aloy Ejimakor, lauyan Nnamdi Kanu, ya ce bukatar ta sake yin watsi da shari’ar ya fito ne daga wanda yake karewa.
Nnamdi Kanu, wanda ke hannun hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) tun shekarar 2021, yana gurfana a gaban Misis Nyako bisa zargin ta’addanci da cin amanar kasa da ke da nasaba da fafutukar neman ballewa daga kasar a matsayin mai fafutukar kafa kasar Biafra.
Ya isa harabar kotun ne tare da jami’an tsaro na DSS da misalin karfe 8:30 na safiyar ranar Litinin