![]() |
Cristiano Ronaldo |
Shaharren dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr, Cristiano Ronaldo ya bayyana kansa a matsayin dan wasa mafi kyawu a tarihin kwallon kafa.
A wata hira da yayi da La Sexta, Ronaldo ya bayyana cewa wasu za su iya cewa abokin hamayyar sa Lionel Messi, ne dan wasan da yafi kowa da tsohon dan wasan Brazil Maradona.
Sai dai duk da haka, ya ayyana kansa a matsayin dan wasa mafi cikakken tarihi da shahara, yayinda a yanzu kwallayen da yake da su suka tasar ma 925 a makonnan,wanda ya ce zuwa nan da wani dan lokaci kwallayen za su kai 1000.