Nan da 2030 Nijeriya na fatan hako danyen mai ganga milyan 4 kowace rana



Mai bai wa shugaban NIjeriya Bola Tinubu shawara kan makamashi Olu Verheijen, ta ce gwamnatin kasar na kokarin ganin ta cimma burinta na fitar da ganga milyan 4 kowace rana zuwa shekara ta 2030.

Da take zantawa da gidan talabijin na Arise, Verheijen ya ce gwamnatin na janye wasu dokoki masu tsauri domin bai wa kamfunnan kasashen waje damar dawowa don ci gaba da hako danyen man.

Haka kuma ta ce gwamnati za ta karfafa kamfunnan cikin gida domin cimma burinta.
 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp