Na yi nadamar yi wa Tinubu yakin neman zabe a 2023 – Dan Bilki Kwamanda

Abdulmajid Dan Bilki Kwamanda


Dan siyasa kuma jigo a jam’iyyar APC, Abdulmajid Dan Bilki kwamandan ya bayyana cewa ya yi nadamar yakin neman zaben shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu a zaben 2023.

Dan Bilki Kamanda ya bayyana haka ne a yayin zantawar sa da Daily Trust ta wayar tarho, ya ce bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa, Shugaba Tinubu ya gaza wa ‘yan Nijeriya da dama da suka zabe shi a 2023. 

Ya bayyana cewa a duk a rayuwarsa bai taba nadamar wani mataki da ya dauka ba kamar yadda yake nadamar yakin neman zaben Shugaba Tinubu. 

A cewar sa duk da dan jam’iyyar APC ne, amma dole ya yarda cewa gwamnatin Nijeriya karkashin jam’iyyar APC ta gaza, kuma a matsayinsa na wanda ya sadaukar da lokacinsa da dukiyarsa wajen jawo hankalin mutane su zabi jam’iyyar, yana nadamar wannan abu da ya yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp