Dan majalisa mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya, da Bunkure a majalisar wakilan Nijeriya, Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya yi watsi da dakatarwar da aka yi masa daga jam’iyyar NNPP a Jihar Kano.
Da yake mayar da martani kan sanarwar dakatarwar da shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya fitar, Kabiru Alhassan Rurum ya ce shi da takwarorinsa da aka dakatar ba su taba bin bangaren da suka sauya tambarin jam’iyyar ba, yana mai jaddada cewa suna cikin jam’iyyar ta asali.
A baya dai Alhassan Rurum da Aliyu Sani Madakin Gini sun fito fili sun ware kansu daga tafiyar Kwankwasiyya tare da jaddada kansu a cikin Jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.
Category
Siyasa