MKO Abiola ne ya lashe zaben ranar 12 ga watan Yuni - IBB

 


Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce marigayi Basorun Moshood Kashimawo Olawale Abiola ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

IBB ya bayyana hakan ne a cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna “A Journey in Service” wanda aka kaddamar a Abuja ranar Alhamis.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo wanda ya duba littafin ya ruwaito Babangida na cewa Marigayi MKO Abiola ne ya samu rinjayen kuri’u a lokacin zaben.

Idan zaku tuna abaya dai tsohun shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karrama Abiola da lambar girma ta GCFR.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp