![]() |
Bello Muhammad Matawalle |
Minista Matawalle ya yi Allah wadai da kalaman da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya yi a kwanakin baya kan burin shugaban kasa Bola Tinubu a 2027.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike ya fitar ranar Litinin dinnan a Abuja.
Matawalle ya jaddada cewa shugaba Tinubu ya yi abin yabawa a harkokin mulki kuma Babachir Lawal da mukarrabansa za su yi mamakin irin dimbin goyon bayan da shugaban kasar zai samu daga Arewa.
Ya ce shugaban ya yi abubuwan ci gaba a fannoni daban-daban kamar tsaro, tattalin arziki, ababen more rayuwa da kuma harkokin mulki.