Masu shigo da man fetur a Nijeriya sun koka kan rage farashin man fetur da matatar man Dangote ta yi
Jaridar Punch ta rawaito cewa, wasu daga cikin masu shigo da man fetur sun ce an tilastawa musu sayar da mai kasa da farashinsu saboda masu sayen man fetur din za su saya ne kawai a inda mai yake da arha.
A ranar Larabar da ta gabata ce matatar man Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga Naira 890 zuwa Naira 825 kan kowace lita,kuma ragin zai fara ne 27 ga watan Fabrairu.
annan ne karo na biyu da matatar man ta Dangote ta rage farashin man a cikin shekarar 2025.