Yayin da farashin kayan abinci dangin su shinkafa, masara, gero da dawa ke kara sauka a Najeriya manoma sun koka kan halin da suka shiga a yanzu haka.
Saukar farashin kayan na dada saka fargaba ga manoman da ke ganin hakan zai sa mutane da dama kauracewa fannin na Noma da kasuwancinsa, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A wani rahoton hukumar Kididiga ta Najeriya NBS, ta fitar a baya-bayan nan ta tabbatar da cewar an samu saukin hauhawar farashin kaya tun daga watan Disambar 2024 daga 39.84, da ya kai 26.08 a watan Janairun 2025.
Category
Labarai