![]() |
Shugaba Tinubu da 'yan majalisar zartaswa |
Ministan ayyuka Injiniya Dave Umahi ne ya bayyana hakan bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Umahi ya ce yayin da ake ci gaba da sashe na daya da sashe na biyu na babbar hanyar gabar tekun jihar Legas da Ogun, shugaban kasar ya ba da umarnin a fara aiki kan babbar hanyar Calabar da Akwa Ibom.
Ya ce, zuwa yanzu ana ci gaba da gudanar da ayyuka tsakanin jihohin Legas da Ogun,kuma shugaba Tinubu ya bayyana farin cikin sa bisa yadda ayyukan suke tafiya shiyasa ya sahale da fara babbar hanyar.