Majalisar wakilan Nijeriya za ta gayyaci shugaban hukumar zabe INEC kan jinkirin gudanar da zaben cike gurbi na 'yan majalisar tarayya da na jihohi

 

Farfesa Mahmood Yakubu

Majalisar wakilan Nijeriya ta umurci kwamitinta mai kula da harkokin zabe da ya gayyaci shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Mahmood Yakubu da ya gurfana a gabanta domin bayyana dalilan da ya janyo jinkirin gudanar da zaben cike gurbi na 'yan majalisun tarayya da na jihohi.

Majalisar ta cimma matsayar ne yayin zamanta na ranar Talata bayan amincewa da kudirin da dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Bogoro/Dass/Tafawa Balewa a jihar Bauchi, Jafaru Leko ya gabatar.

Da yake magana kan sashe na 68 na kundin tsarin mulki wanda akai wa kwaskwarima a 1999, dan majalisar ya ce tilas ne a bayyana kujerun wa'yanda za su sake zabe da wa'yanda suka mutu a matsayin ba kowa akai, yana mai jaddada cewa sashe na 76(2) cikin baka ya tanadi gudanar da zaben cike gurbi bayan wata daya da samun gurbin da aka rasa ko ake bukatar sake zabe a wasu akwatunan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp