![]() |
Majalisar wakilan Nijeriya |
Majalisar wakilai za ta fara muhawara kan kudirin dokar haraji da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa majalisar domin tantancewa da kuma amincewa.
A ranar 30 ga watan Nuwamban shekarar 2024, ne dai majalisar ta dakatar da muhawarar da ta ke shirin yi kan kudurorin har zuwa wani lokaci bayan adawa da wasu sassan kudurorin da ’yan majalisar wakilai daga yankin arewacin kasar suka yi.
Kamar yadda a wancan lokacin gwamnonin jihohin Arewa suka yi kakkausar suka ga wasu sassan kudurorin dokar.
Sai dai wani dan majalisar daga cikin jahohin shiyyar Arewa maso Yamma ya bayyana wa Daily Trust a ranar Talata cewa , an shirya ci gaba da gudanar da ayyukan majalisa kan kudirorin dokar, kuma shi ne babban batu kan takardar umarni na majalisar wakilai na zaman majalisar a yau, Laraba.