![]() |
'Yan majalisar wakilai |
Wannan ya biyo bayan amincewa da kudurin dan majalisar wakilai Obuku Offorji ya gabatar a zauren majalisar a ranar Talata.
Da yake gabatar da kudirin, ya tunatar da cewa, bayan taron masu ruwa da tsaki a ranar Laraba, 8 ga watan Janairu, ministan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba kamfanonin sadarwa a Nijeriya za su kara farashin kudin sadarwa.
A cewar ministar, ana ci gaba da tuntubar juna tare da wasu kamfanonin sadarwa a kasar kan karin kudin.
Sai dai ya ce ba za a yi karin kashi 100 ba, kuma hukumar NCC za ta amince da sabon tsarin da za a sanar a gaba.