Majalisar dattawan Nijeriya ta kara wa bangaren lafiya kudi da suka kai naira biliyan N300 a cikin kasafin kudin 2025 da aka amince da shi, domin cike gibin janye tallafin da kasar Amurka ta yi.
An dauki wannan matakin ne a jiya Alhamis yayinda majalisar ta amince da kasafin kudin naira tiriliyan 54.9.
Majalisar ta ce wannan karin zai taimaka wa kasar wajen karfafa bangaren kiyon lafiya domin magance kalubalen da za a samu sakamakon janye tallafin kiyon lafiya da kasar Amurka ta yi.
Category
Labarai