Mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu ya caccaki ƙasar Canada saboda ta hana wa manyan sojojin Nijeriya takardar visa


Mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro Nuhu Ribadu ya caccaki ƙasar Canada saboda ta hana wa babban hafsan sojojin Nijeriya Janar Christopher Musa da wasu manyan sojoji takardar visa domin shiga kasar.

Ribadu, wanda ke jawabi a wurin lackar da cibiyar horaswa kan sha'anin tsaro ta shirya a Abuja, ya bayyana matakin a matsayin cin fuskar Nijeriya.

Martanin da zuwa ne bayan da Janar Christopher Musa ya bayyana yadda hukumomin kasar Canada suka hana masa shiga kasar tare da wasu manyan jami'ai.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp