Likita daya ke kula da lafiyar masu lalurar "cancer" 1,800 a Nijeriya - Kungiyar masu dauke da 'cancer ta kasa'

 


Shugaban kungiyar, Farfesa Abidemi Emmanuel Omonisi, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan taron tunawa da ranar cutar "Cancer" ta duniya. 

Farfesa Omonisi ya ce rashin samun isasshen albashi, da rashin tsaro, rashin tsarin kiwon lafiya ingantacce, sune suka haifar da fitar likitocin cutar "Cancer", likitocin manyan cututtuka,da malaman jinya zuwa kasashen ketare.

Ya kara da cewa saboda karancin likitocin da ke kula da masu cutar zuwa yanzu karuwa take yi,kuma ana samun dogayen layuka asibitocin da ake kula da masu cutar ta "Cancer" a fadin kasar.

Sai dai yi kira ga shugabanni a Nijeriya da su magance abinda ke sa kwararrun ma'aikatan lafiya a kasar ke yin gudun hijira zuwa wasu kasashen.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp