Lassa Fever ta yi ajalin mutane 70 cikin wata daya a Nijeriya

 


Cutar Lassa fever ta yi sanadiyar mutuwar mutan 70 a wannan shekarar 2025, mafi yawa daga jihohin Taraba, Ondo da Edo.

Acewar hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta Nijeriya NCDC, a farkon shekarar nan kawai mutane 1, 552 aka yi tunanin sun kamu da cutar, inda mutum 358 aka tabbatar da ita a jikinsu, haka kuma mutum 70 suka mutu sanadiyar cutar wadda ke yaduwa daga beraye.

Jaridar Dailytrust ta gano cewa an samu mutum daya da ya kamu da cutar a kananan hukumomi 58 cikin jihohi 10 na kasar.


Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp