Kungiyoyin Arsenal da Liverpool sun tuntubi Atalanta kan yuwuwar daukar dan wasa Ademola Lookman a kakar wasa mai zuwa

Ademola Lukman

Arsenal da Liverpool sun tuntubi Atlanta kan yiwuwar daukar dan wasan Nijeriya mai shekaru 27, Ademola Lookman daga kungiyar da ke buga Seria A, kamar yadda  thehardtackle.com ta rawaito.

A cewar wani rahoto daga Sacha Tavoleri Lookman na iya komawa gasar Premier a lokacin kakar wasa mai zuwa.  Arsenal da Liverpool na daga cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan na Atalanta bayan wata cacar baka da sukayi da Gian Piero Gasperini kan zubar da Fanareti da dan wasan ya yi a makwannin da suka gabata a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

Lookman na daya daga cikin mafi kyawun 'yan wasa a Seria A tun lokacin da ya koma Atalanta daga RB Leipzig, a watan Agusta 2022.

Sai dai Arsenal ta bayyana sha'awarta na daukan dan wasan gaban,bisa bukatar da take da shi tun bayan da wasu daga cikin 'yan wasan gaban ta suka samu rauni.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp