Kungiyar SERAP mai fafutikar yaki da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta kai shugaban kasa Bola Tinubu kotu kan zargin daukar mataki kan wasu 'yan kwangila da suka karbi sama da naira biliya N167bn daga ma'aikatun gwamnati ba tare da yin aikin da aka tsara ba.
Karar wadda SERAP ta shigar a kotun tarayya dake Lagos, ta sanya ministan shari'a kuma babban lauya na kasa Lateef Fagbemi, SAN a cikin sunayen wadanda ake kara.
Wata sanarwa da mataimakin daraktan SERAP Kolawole Oluwadare ya fitar, ta nemi kotun da ta umurci Shugaba Tinubu da ministan kudi da tattalin arziki Wale Edun, su bayyyana sunayen 'yan kwangilar ga duniya kuma su tabbatar an gurfanar da su gaban shari'a.
Category
Labarai