![]() |
Gwamnonin Arewa maso yamma da wakilan MDD |
Da yake jawabi bayan kammala taron a Abuja, shugaban kungiyar, Gwamnan jihar Katsina,Dikko Umaru Radda ya bayyana cewa sun amince su ba da fifiko wajen wajen kare al’umma, bayar da ilimi da samar da abinci.
Ya bayyana cewa gwamnan Kaduna Uba Sani dana Zamfara Dauda Lawal ,Sokoto Ahmed Aliyu,Jigawa Umar Namadi sun halarci taron, wanda suka samu bayanai daga mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed da Kodinetan Majalisar Dinkin Duniya, Malick Fall,akan ci gaba tare da shirye shirye daban daban da karfafa hadin gwiwa tsakanin MDD da yankin.
Ya kuma bayyana cewa tattaunawa da bankin na AfDB ya mayar da hankali ne kan shirin bunkasa noma a Nijeriya wanda ya shafi jihohin Arewa maso Yamma.
Ya kara da cewa aiwatar da wannan shiri, zai kawo ci gaban aikin noma tare da inganta rayuwar al'ummar da ke yankin.