![]() |
Auwal Ibrahim Sansani |
Shugaban kungiyar Northern Youth Forum Auwal Ibrahim Sansani ya kalubalanci sukar da kungiyar tuntuba ta Arewa wato ACF ta yi game da kalaman shugaban jam'iyyar APC na kasa Dr. Abdullahi Umar Ganduje na cewa duk mai bukatar takarar shugaban kasa daga Arewa ya hakura har sai Tinubu ya kammala shekarunsa 8.
A wata sanarwar da Auwal Ibrahim ya fitar ya ce sun rasa me yasa kungiyar ACF din ta ke kin Shugaban kasa Bola Tinubu duk kuwa da kokarin da yake na dora Nigeria a turbar ci gaba.
" Dama kungiyar ACF ta dade tana nuna cewa ba zata goyi bayan Tinubu a zaben shekara ta 2027 ba, saboda a baya tsahon dakataccen shugaban kungiyar Mamman Osuman ya fito karara ya bayyanawa duniya cewa a 2027 ba za su goyi bayan duk dantkarar da ba daga Arewa ya fito ba, wanda hakan tasa kungiyar ta ce ta dakatar da shi daga mukaminsa". Inji Auwal Ibrahim Sansani
Ya ce duk da kokarin da Tinubu ya ke na inganta tattalin arzikin Nigeria da dora kasar a turbar cigaba, amma sun fahimci tuni kungiyar ACF ta tsayar da matsayarta.
" Ya kamata ACF ta sani da yawa daga cikin yan Arewa za su barawa Tinubu baya, sabani da matakin da kungiyar ta dauka, wanda ba ya daga cikin manufofin da su ka sanya aka kafa kungiyar ta ACF". Auwal Ibrahim Sansani
Shugaban kungiyar Northern Youth Forum ya ce kamata ya yi kungiyar ACF ta marawa Tinubu baya domin ya sami nasarar da ya sanya a gaba wajen kawo aiyukan cigaba Jihohin Arewacin Nigeria.
Ya ce Shugaban kasa Bola Tinubu shi ya kamata yan Arewa su sanya a gaba saboda manufofin ciyar da yankin gaba da yake da su.